IQNA

21:11 - January 06, 2019
Lambar Labari: 3483290
Bangaren kasada kasa, cibiyar Azhar wadda ita ce babbar muslunci a kasar Masar ta yi Allawadai da saka bama-bamai a majami’ar Abu Saifain da ke Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Sky News ta bayar da rahoton cewa, a jiya wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun sanya wasu bama-bamaia cikin jami’ar Saifain da ke unguwar Nasra  cikin birnin Alkahira, wanda ya tarwatse a lokacin da wani babban jami’in ‘yan sanda mai suna Mustafa Ubaid yake kokarin kwance bama-baman.

Rahoton ya ce a na take jami’in ‘yan sanda ya kwanta dama, yayin da wasu daga cikin jami’an tsaro da ke wurin suka samu raunuka.

Cibiyar Azhar ta ce babbar manufar hakan ita ce kawo sabani tsakanin musulmi da kiristoci da suke zaune lafiya da juna a kasar Masar tun fiye da shekaru dubu da dari uku da suka gabata a kasar Masar.

Ita ma a nata bangaren majami’ar kiristocin ta fitar da nata bayanin, inda ta yi alhinin rasuwar babban jami’in ‘yan sandan a kokarinsa na ganin ya kwance bama-baman da aka dana a wurin ibadarsu.

3778732

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، Masar ، Allawadai ، bama-bamai ، kamfanin dillancin labaran iqna ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: