IQNA

23:30 - January 07, 2019
Lambar Labari: 3483292
Bangaren kasa da kasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qsemi ya mayar da Martani dangane da kalaman da Trump ya yi a kan kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yau a birnin Tehran, Bahram Qasemi ya abbayana kalaman da Trump a kan Iran da cewa, wani abu ne da Trump yake fata  amma kuma sai yake bayyana shi tamkar ya faru.

Ya ce ko shakka babu kasar Iran za ta ci gaba da kasancewa a duk inda ya kamata, kuma matsin lambar Amurka ko takunkuminta ba zai hana Iran ci gaba da gudanar da harkokinta, bilhasali ma hakan yana kara mata karfin dogaro da kanta ne.

Haka nan kuma ya kirayi Donald Trump da yake yin tunani kan siyasarsa wadda ba za ta kai kasarsa ko’ina ba, domin matsalarsa ba da Iran ce kawai ba, matsalarsa da dukkanin kasashen duniya ce, har ma da kawayen Amurka daga ciki.

A ranar Lahadin da ta gabata ce Trump ya yi da’awar cewa, daga lokacin daya mulkin kasar Amurka ya ladabtar da Iran, kuma yanzu ba ta iya yin komai a yankin gabas ta tsakiya.

3779162

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: