IQNA

23:32 - January 07, 2019
Lambar Labari: 3483293
Bangaren kasa da kasa, an kammala gasar kur’ani ta kasa da aka gudanar a tarayyar Najeriya karo na 33.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Independent ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, an kammala gasar a garin Gombe, tare da halartar jami’an gwamnati da kuma malamai.

Muhammad Yalwa shugaban kwamitin gasar ya bayyana cewa, mutane 344 ne suka halarci gasar daga jahohi 35 na kasar.

A wannan karon gasar ta gudana a bangarori daban-daban, daga ciki kuwa har da tarjamar ayoyin kur’ani bayan karanta su, inda Zainab Muhammad Paris daga Adamawa ta zo ta daya a bangaren mata, sai kuma Tijani Goni Danbaba daga Yobe ya zo na daya a bangaren maza.

Kowanne daga cikinsu ya samu kyautar kudi Naira dubu 500, kamar yadda kuma za su wakilci Najeriya a gasar kur’ani ta Saudiyya da Kuwait.

3779168

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: