Kmafanin dillancin labaran iqna, ya nakalto ministan cikin gida na kasar ta Sudan yana fadar haka a jiya Litinin.
Ministan ya kara da cewa mutane sha tara ne suka rasa rayukansu tun lokacinda aka fara tashe-tashen hankulan a shekarar da ta gabata.
Amma majiyar kungiyar Amnesty International tana cewa an kashe mutane kimani arba’in a rahoton da ta tattara daga kafafe masu amince a kasar ta Sudan.
Tun ranar sha tara ga watan Decemban da ta gabata ce mutanen kasar sudan suka fara zanga-zangar yin alllawadai da karin farashin kayakin abinci musamman bredi a kasar.
Mutanen kasar sudan dai suna bukatar shugaban Umar Hassan Albashir ya kawo karshen shugabancuin kasar da yake yi tun shekaru talatin da suka gabata.
A bisa tsarin mulkin kasar Sudan a halin yanzu dai shugaban zai kawo karshen mulkinsa a kasar ne a shekara mai zuwa.