IQNA

22:49 - January 09, 2019
Lambar Labari: 3483300
Mahjalisar dokokin kasar India ta amince da wani daftarin kudiri da ke nuna wariya ga musulmi da aka gabatar mata.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, majalisar dokokin kasar India ta amince da daftarin kudirin, wanda ya amince da a bayar da izinin zama dan kasa ga mabiya wasu addinai a kasar 'yan kasashen ketare, amma ban da musulmi.

Daftarin dokar dai na da nufin ganin an bayar da izinin zama dan kasa ga mabiya addinan Hindus, Sik da kuma kiristanci da suka fito daga kasashen Bangaladesh, Pakistan da kuma Afghanistan, matukar sun zauna cikin India fiye da shekaru shida, amma wannan doka ba ta shafi musulmi ba.

Kafin wannan daftarin kudiri da majalisar wakilan kasar India ta amince da shi ya zama doka, sai an mika shi ga majalisar dattijan kasar domin ta kada kuri'a a kansa.

Mabiya addinin muslunci a kasar ta India sun nuna takaicinsu matuka dangane da wannan mataki, inda suke ganin firayi ministan kasar ta India Narendra Modi, ya yi hakan ne da nufin samun kuri'u a zaben da za a gudanar a cikin watan Mayun wannan shekara.

3779774

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: