IQNA

22:06 - January 10, 2019
Lambar Labari: 3483304
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Masar na shirin aiwatar da wani shiri na karfafa makarantun kur’ania  fadin kasar da nufin yaki da jahilci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Masar karkashin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar, na shirin aiwatar da wani shiri na karfafa makarantun kur’ania  fadin kasar da nufin yaki da jahilci musamman a yankuna na karkara.

Bayanin da ma’aikatar kula daharkokin addinin ta kasar Masar ta fitar ya ce, har yanzu akwai wasu yankuna da mutane basu bayar da muhimmanci ga ilimin zamani a cikion kasar ta Masar.

A kan domin magance matsaloli na ilimin zamani, za  akarfafa makarantun kur’ani a yankuna karkara musamman, inda mutane sukan sanya ‘ya’yansu domin koyon karatun kur’ani, inda za a rika hadawa da karatu na zamani.

Bayanin y ace wannanzai taimaka matuka wajen rage samun mutane da suke tasowa ba tare da sun san ilimin zamani ba, kamar yadda kuma zai taimaka ma makarantun kur’ani wajen kara bunkasa a kasar.

                                                                                                             3780079

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، mutane ، tasowa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: