IQNA

22:46 - January 11, 2019
Lambar Labari: 3483305
Ana ci gaba da nuna hotuna a cikin ginin majalisar kungiyar tarayyar turai da ke birnin Brussels na kasar Belgium dangane da mawuyacin halin da matan musulmi na Rohingya suke ciki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, tun a ranar Talata da ta gabata ce aka fara gudanar da wannan baje kolin hotunan matan na Rohingya da nufin tunawa duniya halin da wadannan mutane suke ciki.

Nushina Shahin Mubarak 'yar majalisar cea  majalisar kungiyar tarayyar turai, wadda tana daga cikin wadanda suka shirya shirin, ta bayyana cewa, babbar manufar nuna wadannan hotun ada aka girke a cikin farfajiyar majalisar kungiyar tarayyar turai shi ne, tunatar da wannan majalisa da kuma kasashen turai da na duniya baki daya kan cewa, har yanzu al'ummar Rohingya suna cikin matsala.

Ta ce musamman mata daga cikinsu, wadanda sune suke kula da yara da sauran hidimomi, musamman wadanda aka kashe mazajensu, wadanda basu da wani mai taimako.

A shekarar da ta gabata ce dai Nushina Shahin Mubarak ta kai ziyara a kan iyakokin Myanmar da Bangaladesh, inda aka tsugunnar da dubban daruruwan musulmi 'yan kabilar Rohingya, wadanda suka tsere daga yankuannsu a cikin yanamr, sakamakon kisan gillar da jami'am sojin gwamnatin kasar ke yi a  kansu.

3780250

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: