IQNA

22:51 - January 11, 2019
Lambar Labari: 3483307
Mai magana da yawun Kiristocin kasar Masar na Kibdawa ne ya sanar da cewa an gano wani bom a kusa da majami'ar garin Alexandria kuma an lalata shi

Kamfanin dillancin labaran iqna, paul Halim ya fadawa manema Labaru cewa; Jami'an tsaron kasar Masar ne su ka gano bom din da aka aje da tazarar mita 20 daga majami'ar da ke yankin Smoutha da garin Alexandria tare kuma da lalata shi.

Kakakin kungiyar Kiristocin na Kibdawa ya kara da cewa; Wasu mutane ne wadana ba a tantance su ba su ka ajiye bom din a kusa da majami'ar

A ranar 5 ga watan nan na Janairu ma dai an dasa wani bom a cikin majami'ar da ke gabacin birnin alqahira wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda da jikkata wasu uku

Da akwai kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar ta Masar wadanda suke yawaita kai hare-hare mabiya addinin kirista da majami'oinsu.

3780248

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، Iskandariya ، majamia
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: