IQNA

23:50 - January 12, 2019
Lambar Labari: 3483308
Kasar Iran za ta bude wata makarantar sakandare ta musulunci a kasar Uganda a daidai lokacion da ake gudanar da tarukan cikar shekaru 40 da samun nasarar juyi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Cibiyar yada al'adun muslucni a  kasar Iran ta sanar da cewa, an kammala aikin gina wata babbar makarantar sakandare ta musulucni a   birnin Kampala fadar mulkin kasar Uganda, wanda Iran ta dauki nauyin ginawa.

Bayanin ya ce za a bude makarantyar ne a cikin watan Fabrairu mai kamawa, a lokacin bukukuwan cikar shekaru 40 na samun nasarar juyin juya halin muslucni a kasar ta Iran.

Jakadan Iran kasar Uganda Muhamamd Ridha Qazlasqi da kuma wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar ta Uganda daga bangaren ma'aikatar ilimi da kuma ma'aikatar bunkasa al'adu za su halarci taron bude makarantar.

Wannan makaranta dai baya ga ilmomin addinin musulunci, za a rika koyar da sauran ilmomi na zamani, ta yadda shahadar makarantar za ta zama karbabbiya kamar sauran shahadar makarantun sakandare na kasar Uganda.

Kasar Uganda da ke gabashin nahiyar Afrika, na daya daga cikin kasashen da suke da kyakyawar alaka ta doflomasiyya da kasar Iran ta Iran.

3780393

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Uganda ، Iran ، Kampala
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: