IQNA

23:52 - January 12, 2019
Lambar Labari: 3483309
Bangaren kasa da kasa, majiyoyin tsaro a kasar Burkina Faso sun akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-haren ta’addanci da aka kai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar, ta bayyana cewa an kai hare-haren ne a kasuwan Jasiliki da ke cikin gundumar Soum da ke arewacin kasar, a lokacin da muaten suke cikin kasuwa a daren Juma’a, inda aka kasha mutane 12, dukkaninsu fararen hula.

Bayanin ya kara da cewa, wasu ‘yan ta’adda su 30 daga cikin kungiyoyin masu da’awar jihadi suka kai farmakin dauke da manyan makamai, inda suka firgita jama’a da kuma tarwatsa su, kuma sace dukiyoyin jama’a da ke wurin.

Sakamakon matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankunan arewacin kasar Burkina Faso, musamman hare-haren ta’adda masu dawa’ar jihadi, wannan ya sanya a watanni baya gwamnatin kasar ta kafa dokar ta baci a waddannan yankuna, kuma a jiya an kara sabunta dokar.

Tun a cikin shekara ta 2015 ne dai kasar Burkina Faso ta fara fuskantar hare-haren ta’addanci, inda ya zuwa irin wadannan hare-hare sun yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 270 a kasar.

 

3780446

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: