IQNA

23:55 - January 12, 2019
Lambar Labari: 3483310
An gudanar da taron tunawa da babban malamin addinin muslucni na kasar saudiyya Sheikh Nimr wanda mahukuntan kasar suka yi masa kisan gilla.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a jiya ne wasu kungiyoyin masu fafutuka da masana a kasar Birtaniya suka shirya gudanar da zaman taro na tunawa da babban malamin addinin muslucnci dan kasar saudiyya Sheikh Baqir Nimr Nimr, wanda ya yi shahada shekaru uku da suka gabata, bayan da mahukuntan masarautar Al saud suke sare masa kai da takobi.

Masu gudanar da taron sun hada da kungiyoyin farar hula da lauyoyi da kuma malaman jami'a, gami da wasu daga cikin siyasa masu adawa da salon siyasar masarautar mulkin mulukiya ta Alsaud.

Babban abin da zaman fi mayar da hankali a kansa shi ne, irin gudunmawar da sheikh Nimr ya bayar wajen kara fadakar da mutane kan hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu na 'yan kasa, kamar yadda kuma bai taba ja da baya ba wajen kalubalantar mulkin kama karya.

Haka nan kuma taron bayyana malamin matsayin gwarzo da tarihin kasar ta Saudiyya da ba za a taba mantawa da shi ba.

3780372

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: