Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai Amasa ya bayar da rahoton cewa, a baje kolin kayan tarihi da ke gudana a lardin Khanshala a kasar Aljeriya, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki da ake danganta shi da shekaru 1000 da suka gabata.
Wanda yake mallakar wannan kwafin kur’ani ya bayyana cewa, sun gaje shi ne tun kaka da kankanni, kuma kur’anin yana nan tun lokacin hijirar Amazigawa daga yankin Saqiyyah Hamra.