IQNA

Kira’a Mafi Jimawa A Gidan Radiyin Kur’ani A Saudiyya

20:42 - January 17, 2019
Lambar Labari: 3483321
Bangaren kasa da kasa, gifan tadiyon kur’ani na kasar Sudiyya ya fitar da wata kira’a wadda itace mafi jimawa a gidan radiyon.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na yanar gizo na Rafha cewa, ma’ikatar yada labarai ta kasar Saudiyya ta bayyana kira’ar da aka farwa sanyawa  agidan radiyon kur’ani na kasar da cewa ita ce mafi jimawa.

Wannan kira’a an yi ta ne tun shekaru 48 da suka gabata, kuma sheikh Abdullah Khayyat ne ya yi karatun a lokacin a wannan gidan radiyo.

Marigayi Sheikh Abdullah Khayyat ya yi wannan karatu daga aya ta 203 zuwa ta 208 a cikin surat Baqara a shekara ta 1970, kuma har yanzu ana ci gaba da adana wannan sauti.

3782125

 

 

 

 

captcha