IQNA

20:05 - January 31, 2019
Lambar Labari: 3483341
Bangaren kasa sa da kasa, dubban mutane sun tsere daga hare-haren ta’addancin kungiyar Boko Haram daga Najeriya zuwa Kamaru.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, sakamakon harin Boko Haram dubban mutane sun tsere daga hare-haren ta’addancin kungiyar Boko Haram daga Najeriya zuwa Kamaru a cikin ‘yn kwanakin nan.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majaliasar dinkin duniya ta bayar da rahoton cewa, ‘yan ta’addan sun kai hari a gari Rann da ke cikin Najeriya, inda mutane fiye da dubu talatin suka tsere zuwa cikin Kamaru.

Mutanen da suka gudu sun ce ‘yan ta’addan sun gargade su da cewa za su dawo, idan uma suka samu wani ba za su saurara mas aba.

Kungiyar Boko Haram ta fara kaddamar da hare-hare a Najeriya tun a cikin shekara ta 2009, inda ya zuwa yanzu sun kashe dubban mutane da sunan jihadi.

3785608

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Najeriya ، boko haram ، musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: