Kamfanin dillancin labaran iqna, an cimma yarjejeniya tsakanin wasu madaba’antun kur’ani na Afrika da kuma kungiyar matasan musulmi ta duniya WAMY kan bugawa tare da raba kwafin kur’anai dubu 120 a tsakanin wasu kasashen Afrika.
Bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar, inda za a fara gudanar da aikin nan ba da jimawa ba, domin tabbatar da cewa an raba wadannan kur’anai kafin nan da watan azumi.
Yarjeniniyar dai ta kunshi buga kwafin kur’anai miliyan 4 wanda za a raba su a tsakanin kasashe dasuka hada har da na larabawa.