IQNA

An Bude Cibiyar Kur’ani Ta Warisul Anbiya A Kamar Mali

23:56 - February 06, 2019
Lambar Labari: 3483353
Bangaren kasa da kasa, tawagar hubbaren Hussaini da ta kai ziyara a kasar Mali ta jagoranci bude cibiyar kur’ani ta Warisul anbiya  akasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Ali Karawi shugaban bangaren kur’ani na hubbaren Hussaini, ya jagoranci bude cibiyar kur’ani ta Warisul anbiya  a kasar da nufinn kara fadada ayyukan kur’ani mai tsarki.

Wannan na zuwa ne a ziyarar da wannan tawaga take kaiwa ne a wasu daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afrika, da nufin ganin an kara karfafa ayyuka a bangaren kur’ni mai tsarkia  dukkanin bangarori.

Haka nan kuma Karawi ya gana da wasu daga cikin malamai na kasar da suka hada da malaman mazhabar ahlul bait (AS) da suke a kasar ta Mali, wadanda suke gudanar da ayyuka a bnagaren ilmantarwa da kuma koyar da ilmominsu.

Ziyarar wannan tawaga  akasar Mali tana zuwa ne bayan kammala ziyarar da wannan tawaga ta kai a kasar Burkina Faso ne, inda  acan ma aka bude wata cibiyar makamanciyar wannan.

3787830

 

 

 

 

 

 

captcha