IQNA

Gwamnatin kasar China Ta lakafa Kamarori Domin Sanya Ido  A Kan Musulmi

23:12 - February 21, 2019
Lambar Labari: 3483393
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar china ta lakafa kamarori a yankin da musulmi suke da zama domin sanya ido a kansu da kuma harkokinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Magrib yaum ya bayar da rahoton cewa, a ci gaba da daukar matakan takurawa kan musulmi, gwamnatin kasar china ta lakafa kamarori a yankin Sing Kiyang na musulmi domin sanya ido a kansu da kuma dukkanin zirga-zirgarsu da sauran harkokinsu na yau da kullum.

Rahoton ya ce wadannan kamarori suna sanya ido a kan musulmi sama da miliyan biyu da rabi da ke yankin, wadanda suke fuskantar gallazawa daga jami’an tsaron gwamnatin kasar ta China.

Yanzu haka akwai miliyoyon muusulmi da China ta tsare a wani sansani tare da hana su gudanar da harkokinsu, inda ake tilasta su cin naman alade da kuma shan giya, kamar yadda a cikin watan azumi ake tilasta su cin abinci da rana.

3792068

 

 

 

 

 

captcha