Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar da ya yi da tashar shams FM a jiya, minister mai kula harkokin addini a kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnatin kasar na shirin ganin ta inganta makarantun kur’ani a kasar.
Yace ko shakka babu ma’ikatarsa ta gudanar da ayyuka masu matukar muhimmanci a cikin lokutan baya-bayan nan, da hakan ya hada da gina makarantun kur’ani mai tsarki.
Haka nan kuma ya yi ishara da ginin sabuwar makarantar kur’ani ta Ibn Umar da ke yankin Alriqab a cikin gundumar Buziz, inda ya ce wannan na daga cikin muhimman ayyukan da suka sanya agaba a halin yanzu.
Furucin na ministan kula da harkokin addini na Tunisia ya zo ne bayan kakkausar sukar da ya sha daga bangarori daban-daban na al’ummar kasar, bayan da ya yi dirar mikiy a kan makarantun kur’ani a baya.