IQNA

19:48 - March 01, 2019
Lambar Labari: 3483415
Wani rahoton majalisar dinkin duniya ya yi nuni da cewa ‘yan gudun hijira na ‘yan kabilar Rohingya na cikin mawuyacin hali a sansanoninsu da aka tsugunnar da su a kasar Bangaladesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, babbar jami’ar majalisar dinkin duniya kan sha’anin rikicin Myanmar Christine Schraner Burgener ta gabatar da rahoto ga majalisar dinkin duniya a jiya, dangane da halin da dubban daruruwan ‘yan gudun hijira ‘yan kabilar Rohingya suke a kasar Bangaladash.

Rahoton ya ce ‘yan gudun hijirar suna cikin mawuyacin hali, kuma suna da bukatar taimako na gaggawa a irin wannan yanayi da suke ciki, musamman mata da kananan yara wadanda su ne suka fi saurin galabaita.

Jami’ar ta ce ta zagaya yankuna daban-daban a inda aka tsugunnar da dubban daruruwar ‘yan kabilar ta Rohingya  acikin bangaladash, kuma dukkanin wurare halin da suke ciki ba mai kyau ba ne, a kan haka ta bukaci da a sake yin dubi kan wannan batu, da kuma dayukar matakan da suka dace domin taimaka wadannan ‘yan gudun hijira.

3794288

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: