IQNA

23:43 - March 06, 2019
Lambar Labari: 3483431
Bangaren kasa da kasa, shugabar kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ta gargadi India kan cutar da musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamafanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a zaman da kwamitin kare hakkin bil adama na majlaisar dinkin duniya ya gudanar a yau a birnin Geneva na kasar Switzerland, shugabar kwamitin Michellr Bachelet ta gargadi India kan cutar da musulmi da take yi.

Ta ce suna cikakkun bayanai kan irin matakanda gwamnatin India take dauka na gallazawa muuslmi a  wasu yankunan kasar, wandaa cewarta hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, kan kare hakkokin marassa rinjaye.

Tace suna gargadin India da ta sake yin nazari kan hakan, domin kuwa za ta cutu matuka sakamakon irin wadannan matakai, kamar yadda hatta tatalin arzikinta zai yi rauni, matukar ta zabi bin salon siyasar dannen marassa rinjaye a kasar tare da cutar da su.

3795869

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: