IQNA

23:54 - March 07, 2019
Lambar Labari: 3483434
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya sun kai samame a masallacin Aqsa ta kofar babul magariba.

Bangaren kasa da kasa, kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa yahudawan sahyuniya sun kai wani samame da jijjifin safiyar yau a masallacin aqsa, inda suka kutsa kai a cikin babul magariba.

Yahudawan share wuri zauna sun kai samamen ne a lokacin da jami’an tsaron Isra’ila suke basu cikakkiyar kariya, domin hana Falastinawa sun kare wurin.

Wannan dai bas hi ne karon farko da ynan wuri mai tsarki ba, domin kuwa a koa  cikin makon da ya gabata sun kutsa kai cikin harabar masallacin mai alfarma.

Al’ummar Palastine dai suna kan bakansu na kin amincewa su mika alkiblar musulmi ta farko ga mamayar yahudawa, wanda hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin kasashen larabawa suke ta hankoron neman samun kusanci da Isra’ila, domin farantawa Amurka.

3796051

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: