Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai Al-sabah ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta sanar da bude cibiyoyin hardar kur’ani guda 70 a fadin kasar kuma yanzu haka mutane 4441 sun yi rijistar sunayensu a cibiyoyin.
Bayanin ya kara da cewa, mafi yawan wadanda suka yi rijistar sunayensua wadannan cibiyoyi dai mata ne, kuma ana sa ran adadin zai ci gaba da karuwa a cikin ‘yan lokuta masu zuwa.
Haka nan kuma yanzu haka ana shirin bude wasu cibiyoyin a biranan Akahira, Sinai ta arewa, Iskandariyya, Diqhaliyya da Suiz.