IQNA

23:55 - March 09, 2019
Lambar Labari: 3483440
Bangaren kasa da kasa, fiye da masallata dubu 40 ne suka yi sallar Juma’a a jiya a masallacin aqsa mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, duk da irin tsauraran matakan da jami’an tsaron yaudawa suka dauka, amma fiye da masallata dubu 40 ne suka yi sallar Juma’a a jiya a masallacin aqsa mai alfarma da kewaye.

Tun kafin wannan lokacin dai jami’amn tsaron yahudawan sun kafa shingayen tsaro da uma bincike, domin hana falastinawa isa cikin masallacin.

Daga cikin irin matakan da suke dauka har da hana matasa da kuma wadanda shekarunsu abs u haura arba’in ba shiga cikin harabar masallacin, amma duk da hakan dubban muuslmi sun samu damar shiga cikin masallacin da harabarsa kuma sun yi sallar Juma’a.

 

3796178

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: