IQNA

22:55 - March 13, 2019
Lambar Labari: 3483455
Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan jin kai a kasar Yemen ta fitar da rahoto dangane da kisan fararen hula 22 da Saudiyya ta yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, Shafin yada labarai na Al-khalij ya bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton da ta fitar, babbar jami'ar majalisar dinkin duniya kan ayyukan jin kai a kasar Yemen Liz Grande ta sanar da cewa, ta bi kadun abin da ya faru dangane da harin da jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar a kauyen Kushar da ke cikin gundumar Hajjaha  raewacin kasar Yemen.

Rahoton ya ce jami'an majalisar dinkin duniya sun ziyarci asibitocin da akja kai gawawwakin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka, inda suka tabbatar da cewa kananan yara 12 da kuma mata 10 ne suka rasu sakamakon harin, yayin da wasu fiye da talatin suka jikkata.

Rahoton na tawagar majalisar dinkin duniya ya kara da cewa, jiragen na Saudiyya sun kai hare-haren ne a kan gidajen jama'a fararen hula, inda babu wani abu da yake da alaka da ayyukan soji, kuma dukkanin wadanda suka rasu fararen hula da ba su san hawa ba su san sauka ba.

 

3797518

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sauka ، Saudiyya ، yemen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: