IQNA

23:54 - March 14, 2019
Lambar Labari: 3483457
Yahudawan sahyuniya ‘yan share wuri zauna sun sake kaddamar da wani farmaki a jiya Laraba a kan masallacin Aqsa mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, yahudawan wadanda suka hada mazauna wasu matsugunnan yahudawa da ke gefen birnin Quds, da kuma wasu dalibai masu karatun addinin yahudanci masu tsatsauran ra’ayi ne suka kai farmakin.

Rahoton ya kara da cewa daruruwan yahudawan suna samun cikakkiyar kariya daga jami’an tsaron Isra’ila a lokacin da suka kutsa kai a cikin harabar masallacin mai alfarma.

Koa  cikin makon da ya gabata ma wasu yahudawan sun kai irin wannan samame a kan masallacin domin tsokanar Falastinawa, inda wasu daga cikin matasan Falastinawa suka hana su shiga cikin harabar masallacin, amma daga bisani jami’an tsaron Isra’ila suka tarwatsa su, tare da kame wasu daga cikinsu.

3797790

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، quds ، falastinawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: