IQNA

23:57 - March 14, 2019
Lambar Labari: 3483458
A daidai lokacin da shugaban kasar Aljeriya ya sanar da cewa ba zai yi ta zarce a kan mulki ba, 'yan siyasa da masu korafi kan takararsa suna ci gaba da kara matsa lamba a kansa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, mataimkain firayi ministan kasar Aljeriya Ramadan La'amamira ya kirayi al'ummar kasar da su kai zuciya nesa, domin samun maslaha da zaman lafiya a kasar baki daya.

Mataimakin Firayi ministan ya yi wannan bayani ne a yau, inda ya ce da dama daga cikin masu korafi suna yin kira ne zuwa ga canjin gwamnati, ya ce wannan shi ne abin da zai faru, domin kuwa matsayar da shugaban kasar Abdulaziz Butaflika ya dauka na nufin hakan, kuma lamari ne da ya cancanci a jinjina masa.

Wanann furuci na La'amamira na zuwa ne bayan da mafi yawa daga cikin masu zanga-zangar kin amincewa da takarar Butaflika  a karo na biyar, suke nuna rashin amincewarsu da daga lokacin zabe, inda suke ganin hakan a matsayin wata hanya ta ci gaba da mulkinsa daga nan har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben.

 

3797818

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، cewa ، zarce ، tsakanin
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: