IQNA

23:58 - March 14, 2019
Lambar Labari: 3483459
Babban kwamitin kare hakkin bil adama na kungiyar tarayyar turai ya bukaci da a yi adalci kan batun kisan gillar da aka yi wa dan jaridar kasar Saudiyya Jamal Khashoggi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya fitar wanda jaridar Washington Post ta buga, shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na kungiyar tarayyar turai Antonio Penzery ya bayyana cewa, har yanzu ana ci gaba da yin rufa-fufa kan batun kisan Jamal Khashoggi.

Ya ce batun kisan Khashoggi ba abu ne da za a yi shiru a kansa ba, domin kuwa yin hakan ba adalci ba ne a gare shi da sauran wadanda ake tauye musu hakkoki a kasar ta Saudiyya., domin kuwa a cewarsa abin da yake faruwa shi ne ana son a rufa wa Muhammad Bin Salman asiri ne a cikin batun kisan, wanda kuma ba abu ne mai boyuwa ba.

Kungiyar leken asirin Amurka ta CIA dai ta bayar da rahoton cewa, Muhammad Bin salman ne ya bayar da umarnin yi wa Khashoggi kisan gilla a cikin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiya, inda ta nadi bayanai na maganganun da suka wakana ta wayar tarho tasakanin makasan Khashoggi da kuma Muhammad Bin Salman kafin aiwatar da kisan, da kuma bayan aiwatar da kisan, amma gwamnatin Trump taki amincewa da hakan, sakamakon harkokin kasuwanci na daruruwan biliyoyin daloli da ke tsakaninsu.

3797635

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، khashoggi ، saudiyyah
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: