IQNA

23:08 - March 15, 2019
Lambar Labari: 3483461
Rahotanni daga New Zeland, na cewa mutum 49 ne suka rasa rayukansu, kana wasu ashirin na daban suka raunana a yayin wasu tagwayen hare haren bindiga da aka kai kan wasu masallatai biyu a yankin Christchurc.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ganau sun bayyana wa masu aiko da rahotanni cewa mafi yawa daga cikin wadanda lamarin ya rusa dasu yara ne da mata.

Da take tabbatar da hakan firaministar kasar ta New Zeland, Jacinda Ardern, ta bayyana lamarin da abun takaici da ba'a taba ganin irinsa ba a kasar.

An dai tantance wani dan asalin kasar Austria mai tsatsauran ra'ayi da hannu a harin.

A halin da ake ciki yan Sanda a kasar ta New Zeland sun capke mutane hudu da ake zargi da hannu a tagwayen hare haren da aka kai a masallatan guda biyu.

Shugaban yan Sandan yankin Mike Bush kuma ce sun yi nasarar kwance wasu bama-bamai.

 

3797972

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bama-bamai ، kwance ، daban ، Newzealand
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: