IQNA

Iran Ta Yi Allawadai Kan Harin Da Aka Kai Wa Musulmi A Newzeland

23:11 - March 15, 2019
Lambar Labari: 3483462
Kakakin ma’ikatar harkokin wajen kasar Iran bahram Qasemi ya bayyana cewa kasar Iran tana yin Allawadai da kakausar murya kan harin da aka kaiwa musulmi a Newzealand.

Kamfanin dillancin labaran iqna,a  cikin wata sanarwa da ya fitar, Bahram Qasemi kakakin ma’ikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana harin da cewa aiki ne na dabbanci da rashin ‘yan adamtaka, domin kuwa wadanda suka aikata haka babu wani abu mai hurumi a wurinsu, domin kuwa sun kasha ‘yan adam a wurin ibada.

Ya ce wannan hari lamari ne mai matukar hadari, domin kuwa abu ne da aka kaddamar a kan muuslmi da suke zaune a wata kasa wadda kare rayukansu da wuraren ibadarsu ya rataya  akanta.

A haka qasemi ya ce ya zama wajibi kan gwamnatin kasar Newzealand da ta dauki matakan gaggauwa wajen gano dukkanin wadanda suke da hannua  cikin wannan aiki na ta’addanci domin su fuskanci shari’a daidai da aikinsu.

An kai hare-haren ne a garin Church Christ da ke kasar Newzealand a kan masallatai biyu na musulmi, inda aka kashe kimanin mutum hamsin bisa ga kididdiga ta farko.

3798009

 

 

captcha