IQNA

Ana Ci Gaba Da Mayar Da Martani Kan harin New Zeland

23:04 - March 16, 2019
Lambar Labari: 3483465
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ta bayar da kakkausan martani dangane da harin da aka kaiwa musulmi a kasar New Zealand.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyar ta fitar a safiyar yau, ta bayyana harin da aka kai wa muuslmi a  cikin masallaci a kasar New Zealand da cewa abin yin Allawadai ne.

Bayanin ya ce ko shakka babu abin da ya faru kan musulmi a  kasar New Zealand yana dauke da sako mai matukar hadari, domin kuwa sako ne na nuna wariya da bambanci tsakanin 'yan adam da kuma addinansu, wanda dol ne duniya tashi tsaye domin kawo karshen hakan, matukar dai ana son zaman lafiya da adalci da sulhu a tsakanin 'yan adam.

A daya bangaren kuma gwamnatocin kasashen duniya suna ci gaba da yin Allawai da wannan hari, da kuma nuna alhininsu ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.

bayan faruruwar lamarin gwamnatocin kasashen Rasha da kuma jamhuriyar muslucni ta Iran, gami da Turkiya, da kuma Indonesia da kuma wasu daga cikin kasashen kasashen musulmi, sun yi Allawadai ad harin.

Ita ma a nata bangaren kungiyar tarayyar turai da majaliasar dinkin duniya sujn fitar da nasu bayanan na yin tir da Allawadai da wadannan hare-hare da aka kaddamar a kan musulmi a kasar New Zealand.

3798010

 

 

 

captcha