IQNA

Rohani Ya Isar Da Sakon Shiga Sabuwar Shekara

23:57 - March 21, 2019
Lambar Labari: 3483479
Shugaban kasar Iran Hassan Ruhani ya taya al'ummar kasarsa murnar shiga sabuwa shekara.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin sakonsa na taya murnar, shugaba Runani, ya ce a cikin sabudar shekara ta 1398, gwamnatinsa, zata dauki sabbin matakai na farfado da darajar kudin kasar.

Haka zalika gwamnatinsa zata samar da hanyoyin kulla hulda tsakanin Teheran da dukkan kasashe makobta.

Shugaba Ruhanin ya kara da cewa matsalolin da kasarsa ke fama dasu duk sun samo tushe ne daga ketare, saboda siyasar zalunci da ta makiyanmu.

Ya ce a yau muna kalubalantar wani matsi da dukkan Iraniyawa ke fada dashi, wanda kuma rashin hadin kai zai zamo mana babban kalubale.

A karshen jawabin nasa, Dakta Ruhani ya mika sakon murnar shiga sabuwar shekara hijira shamsiya ga takwarorinsa na kasashen yankin da suka hada da Afganistan, Tadjikistan, Pakistan, Azerbaijan, Turkmenistan, Armeniya, Kirghiz, kazakhstan, India da kuma Uzbek.

3799335

 

 

 

captcha