IQNA

Sojojin Yahudawa Sun kashe Wani Matashi A Gaza

23:54 - March 24, 2019
Lambar Labari: 3483488
A daren jiya jami'an sahayuniyya sun bindige wani matashin Bapalastine a gabashin zirin Gaza

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto ma'aikatar kiyon lafiya ta Palastinu na cewa a daren jiya  jami'an tsaron Isra’ila sun harbi  wani matashin Bapalastine mai suna Habib Hamzah Misri a kirjinsa da harsasan bindiga  a gabashin yankin zirin Gaza.

A daren na jiya jami'an tsaron Sahayuniyya sun  bude wuta kan wasu Palastinawa da suke zanga-zangar lumana a kan iyakar yankin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutum hudu daga cikinsu akwai Habib Hamzah Misri, inda aka garzaya da su zuwa asibiti, jim kadan bayan zuwa asibitin, Habib Hamzah Misri ya yi shahada.

Har ila yau, jirgin yaki maras matuki na jami'an tsaron Sahayuniyya ya kai farmaki kan wasu matasa a gabashin yankin zirin Gaza, tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu.

A safiyar jiya lahadi ma, jiragen yakin Isra'ila sun yi lugudan wuta a wani wurin bincike na kungiyar gwagwarmayar Palastinawa ta Hamas a kudancin Gaza.

3799556

 

 

 

 

captcha