IQNA

Romania Da Honduras Za Su Mayar Da Ofisoshin Jakadancinsu Zuwa Quds

23:15 - March 25, 2019
Lambar Labari: 3483489
Gwamnatocin kasashen Honduras da kuma Romania sun sanar da aniyarsu ta dauke ofisoshin jakadancinsu daga birnin Tel Aviv zuwa Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na MENA ya bayar da rahoton cewa, gwamnatocin kasashen Honduras da kuma Romania sun bayyana shirinsu na dauke ofisoshin jakadancinsu daga birnin Tel Aviv zuwa Quds domin bin sahun Amurka.

Firayi ministar kasar Romania Viorica Dancila ta sanar da cewa, kasarta ta yanke wannan shawara, kuma za a fara aiwatar da shirye-shiryen hakan kafin fara bababn taron kungiyar yahudawan Amurka AIPAC.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Honduras Juan Orlando Hernandez ya sanar da amincewarsa kan mayar da ofishin jakadancin kasarsa dake Tel Aviv zuwa birnin Quds nan ba da jimawa ba.

Sai a nasa bangaren babban sakataren bangaren zartarwa na kungiyar PLO Sa’ib Uraikat ya bayyana wannan matsaya ta kasashen biyu da cewa ta yi hannun riga da dukkanin ka’idoji da dokoki na diflomasiyyar kasa da kasa.

3799657

 

 

 

captcha