IQNA

Falastinawa Sun Mayar Da Martani Kan Isra'ila Da Makami Mai Linzami

23:17 - March 25, 2019
Lambar Labari: 3483490
Gwamnatin yahudawan Isra'ila ta tabbatar da harba wani makami mai linzami wanda ya sauka a wani matsugunnin yahudawa 'yan share wuri zauna a kusa da birnin Tel Aviv.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau Litinin Falastinawa 'yan gwagwarmaya sun harba wani makamai mai linzami daga yankin zirin gaza zuwa kusa da birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar gwamnatin yahudawan Isra'ila.

Majiyoyin gwamnatin yahudawan sun ce makamain ya sauka a kan wani gina na yahudawa, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar 7 daga cikinsu.

A nasa bangaren Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda ya nufi Amurka domin halartar bababn taron kungiyoyin yahudawa a Amurka, ya sha alwashin daukar mataki kan kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa kan hakan.

Tun kwanaki uku da suka gabata ne jiragen yakin Isra'ila suke ta yin lugudan wuta  akan gidajen Falastinawa a cikin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane a yankin.

 

3799637

 

 

 

 

 

captcha