IQNA

An Raba Kwafin Kur'ani Da Haruffan Brial A haramin Makka

23:50 - March 26, 2019
Lambar Labari: 3483493
Bangaren kasa da kasa da kasa, an raba kwafin kur'ani mai tsarki da aka buga a cikin haruffan Bril a masallacin Makka.

Kamfanin dillancin labaran iqna, babban darakta mia kula da harkokin masallacin haramin Makka mai alfarma ya raba kwafin kur'ani a cikin harufffan Bril ga makafi.

Wanann shiri dai yana zuwa bayan da cibiyar da ke kula da ayyukan harami mai alfarma na makka ta kudiri aniyar sanar da kwafin kur'anai domin amfanin mutane masu fama da larori na musamman.

Makafi na daga cikin wadanda suka fara cin moriyar wannan shiri, wanda kuma a nan gaba za a kara samar da wasu kwafin masu tarin yawa da za a rika a jiyewa a wurare na musamman da aka tandar ga makafi a cikin masallacin harami.

3799629

 

captcha