IQNA

Hare-Haren Jiragen Yakin Isra'ila A Gaza

23:54 - March 26, 2019
Lambar Labari: 3483494
Bangaen kasa da kasa, Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a kan al'ummar Falastinawa mazauna yankin zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tun da jijjifin safiyar yau  Jiragen Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a kan al'ummar Falastinawa mazauna yankin zirin Gaza, tare da rushe gidajen jama'a.

Wadannan hare-hare na zuwa ne bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Hamas da Isra'ila, inda Hamas take ci gaba da yin aiki da tsagaita wuta, yayin da Isra'ila kuma take ci gaba da keta yarjejeniyar.

Rahotanni sun ce jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare har sau 30a  lokaci a cikin yankunan zirin Gaza, inda rusa gidajen jama'a da kuma cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu.

Tun kimanin mako guda kenan da Isra'ila ta fara kaddaamr ad hare-haren neman tsokana  akan Gaza, inda a nasu bangaren kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa suka mayar da martani da makamai masu linzami har zuwa kusa da birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar gwamnatin yahudawan Isra'ila.

3799793

 

captcha