IQNA

Sayyid Nasrulla: Gwagwarmaya Ce Kawai Ce Kawai hanyar Kwato Palastine

23:48 - March 27, 2019
Lambar Labari: 3483497
Bangaren kasa da kasa, shugaban kungiyar Hizbulla sayyid Hasan Nasrullah ya bayyana cewa, al’ummomin Palastine, Syria Da Lebanon suna gwawarmayar ‘yancin kasasensu ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran kungiyar HIzbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana kokarin shugaban kasar Amurka na daukar tuddan Gulan a matsayin wani sashe ha HKI a matsayin cin mutuncin musulmi da larabawa.

Sayyid Hassan Nasarallah wanda ya gabatar da jawabi a marecen jiya Talata ya ci gaba da cewa; Batun tuddan Gulan yana da matukar muhimmanci a rikicin Larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ila, duk kuwa da cewa kasashen larabawa da dama suna kawance da Amurka.

Jagoran kungiyar ta HIzbullah ya kara da cewa; Domin kare Haramtacciyar Kasar Isra’ila, Trump yana sa dokokin kasa da kasa a karkashin kafarsa ya take.”

Sayyid Nasarllah ya kuma ce; Donald Trump ba ya ganin kimar Majalisar Dinkin Duniya balle kudurorinta, gwamnatin Amurka tana amfani da MDD ne idan har hakan zai kare mata manufofi.”

A shekaran jiya Litnin ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana amincewarsa da ikon HKI akan yankin tuddan Gulan na Syria.

Kasashen duniya da dama sun yi watsi da matakin na Amurka tare da bayyana shi a matsayin wanda yake cin karo da dokokin kasa da kasa.

 

3799895

 

captcha