IQNA

Gasar Kur’ani Tana Kara Hadin Kai Tsakanin Musulmi

23:50 - April 16, 2019
Lambar Labari: 3483551
Bangaren kasa da kasa, wanda ya zo na daya a gasar kurani mai sarki ta dalibai a kasar Iran ya bayyana gasar kur’ani da cewa hanya ce ta kara hada kan al’ummar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Abdulalim Abdulrahim Muhammad Haji dalibin da ya zo na daya a gasar kurani mai sarki ta dalibai a kasar Iran ya bayyana gasar kur’ani da cewa hanya ce ta kara hada kan al’umma.

Ya ci gaba da cewa, gasar ur’ani ta kasar Iran ta sha babnban da sauran gasar da ae gudanarwa a sauran kasashen duniya ta bangarori daban-daban, musamman yadda gasar ta Iran ta shafi bangarori hudu.

Na daya shi ne bangaen masu gasa kamar yadda aka saba, sai kuma bangaren dalibai, da kuma bangaren gasar mata zalla, sai kuma gasar kur’ani ta makafi.

An kammala gasar kur’ani ta Iran a jiya tare da halartar makaranta daga kasashe duniya tamanin da takwas, sai kuma alkalai na kasa da kasa.

Da kasar Kenya ne ya zo na daya a bangaren gasar karatu ta dalibai a wannan karo.

3804064

 

 

 

 

 

captcha