IQNA

Rasha: ‘Yan Ta’addan Daesh Sun Samu Mafaka A Afghanistan

23:54 - April 21, 2019
Lambar Labari: 3483566
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Rasha ta ce; ‘yan ta’addan daseh da suka sha kashi a Syria sun tsere zuwa kasashen Afghanistan da Libya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Sputnik ya habarta cewa, ministan tsaron kasar Rasha Sergey Shoygu ya fadi jiya Lahadi cewa, a halin yanzu Afghanistan ta zama wata matattara ta ‘yan ta’addan Daesh da suka tsere daga Syria.

Ya ce ko shakka babu Rasha tana kallon hakan a matsayin wata barazana ta tsaro a gare ta, a kan haka za ta karfafa ayyukan tsaro tsakanin sojojinta  da na kasar Tajikistan, domin fukantar wannan barazana.

A wata ganawa da ta gudana a kwanakin baya tsakanin shugabannin kasashen Rasha da Tajikistan, sun tattauna a kan wajabcin karfafa ayyukan hadin gwiwa na tsaro a tsakaninsu.

Rasha ta bayyana cewa, kasantuwar mayakan Daesh a cikin Aghanistan babbar barazana ce ga dukkanin kasashen yankin, a kan za ta ci gaba da kara hada kan kasashen yankin domin tabbatar da cewa sun fuskanci barazanar ta’addancin Daesh.

3805151

 

 

captcha