IQNA

An Cafke Mutane  Sha Uku Bayan Harin Sri Lanka

21:47 - April 22, 2019
Lambar Labari: 3483570
Rundunar 'yan sandan Sri Lanka ta bayyana cewa, an kama mutane 13 dangane da jerin hare haren bama-baman da aka kai a kasar, a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kawo yanzu dai adadin mutanen da aka rawaito sun rasa rayukansu a jerin hare-haren da aka kai kan majami’u da kuma otel-otel sun lashe rayukan mutane kusan 300 da kuma raunata wasu sama da 500.

Rundunar 'yan sandan kasar, ta ce an mika mutane 10 cikin 13 da aka kama a Colombo, babban birnin kasar ga sashen binciken manyan laifuffuka.

Firaministan kasar Ranil Wickremesinghe ya shaidawa manema labarai cewa, mutanen da aka kama 'yan kasar Sri Lanka ne, ana kuma gudanar da bincike don kara gano wadanda ke da hannu a tashin abubuwan fashewar, duk da cewa kawo yanzu babu wata kungiya da ta dau alhakin kai hare haren.

A halin da ake ciki a kasar dai an katse hanyoyin sadarwa na zamani irin su facebook da kuma watsapp domin kaucewa yada labaren karya ko marassa tushe da kan iya tada zaune tsaye ko kuma tunzura wasu domin daukar fansa.

Adadin mutanen Sri Lanka ya kai miliyan 22, kashi 70 cikin dari na mutanen kasar ‘yan buda ne, kashi13 mabiya addinin Hindus, sai kuma kashi 10 muuslmi, yayin da kashi 7 kuma kiristoci ne.

3805653

 

 

 

captcha