IQNA

A Duk Lokacin Da Amurka Ta Kulla Wani Makirci Ba Ta Yin Nasara

20:17 - April 25, 2019
Lambar Labari: 3483576
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Babu wani abu a gaban Iran idan ba turjiya da tsayin daka ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shugaba Hassan Rauhani ya bayyana haka ne a yau Laraba sannan ya kara da cewa; Amurka karya take yi ba neman tattaunawa take yi da Iran ba.

Rauhani ya kuma ce; A cikin shekaru 40 na cin nasarar juyin musulunci, babu abin da Amurkan take yi idan ba kitsa makirci da makarkashiya ba akan al’ummar Iran, amma kuma ta ci kasa, don haka a wannan karon ma, kasar za ta ci.

Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; A fili yake cewa matsin lamba na tattalin arziki da ake yi wa Iran, yana shafar rayuwar yau da kullum ta mutane, amma a lokaci guda al’ummar Iran ta kwana da sanin cewa babu wani abu da yake a gabanta idan ba tirjiya da tsayin daka ba.

Shugaba Hassan Rauhani ya ce; A ko da yaushe al’ummar Iran tana aiki da diplomasiyya da tattaunawa, amma kuma a lokaci guda ta iya yaki, don haka a shirye take ta kare kanta.

A cikin wannan makon ne dai Amurka ta sanar da cewa; Ta daina dagawa wasu kasashe kafa akan sayen man fetur din Iran.

Kasashe da dama sun yi watsi da matakin na Amurka tare da bayyana shi a matsayin wanda ba zai taimaka ba wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

3806195

 

 

 

captcha