IQNA

Musawi: Babu Wata Kasa da Za ta Maye Gurbin Iran A Kasuwar Mai

22:50 - April 26, 2019
Lambar Labari: 3483579
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa, Iran ba za ta taba bari wata kasa tam aye gurbinta ba a kasuwar mai ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Sayyid Musayi ya yi tir da Allawadai da kakakusar murya kan matakin da gwamnatocin Saudiyya, Bahrain da kuma UAE suka na dauka, na yin mara da takunkumin Amurka  akan kasar Iran, inda kuam suka yi wa Trump alkawalin cewa za su cike gurbin Iran a kasuwar mai ta duniya.

Ya ce wannan ya kara tabbatar da jahilcin wadannan kasashe, wadanda suke yin tunani da kwakwale irin na jahiliyyar larabawa kafin zuwan addinin musulunci wanda ya mayar da su mutane.

Haka nan kuma ya gargadi Amurka da wadannan kasashen da suke mara mata baya da cewa, su ne suke da alhakin dukkanin abin da zai biyo bayan daukar matakin hana Iran sayar da danyen manta  a duniya.

Dangane das are kawunan mutane 37 da Saudiyya ta yi a ranar Talata da ta gabata kuwa, sakamakon ra’ayoyinsu na siyasa, da kin amincewa da tsarin danniya da kama karya na sarakunan kasar, Musawi ya bayyana  wanann matakin da cewa yana tattare da hadari, domin kuwa yana cikin siyasar neman haddasa fitina a yankin gabas ta tsakiya da sunan banbancin mazhaba tsakanin al’ummar musulmi.

Mutane 33 daga cikin wadanda Saudiyya ta sare wa kawuna ‘yan shi’a ne daga yankin gabashin kasar, wadanda aka kama su saboda ra’ayoyinsu an siyasa, amma an kashe su da sunan ‘yan ta’adda.

 

3806417

 

 

 

 

captcha