IQNA

Jami’an Tsaron Masar Sun Ce Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 12

22:40 - May 20, 2019
Lambar Labari: 3483660
Majiyoyin tsaro a kasar Masar sun sanar da kashe ‘yan ta’adda 12 a yankin Jiza na kasar .

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta Alamnar ta bayar da rahoton cewa, ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar Masar ta sanar da cewa, jami’an tsaro sun kai farmakia  wata maboyar ‘yan ta’adda a cikin yankin Jiza, kuma sun samu nasarar kashe 12 daga cikinsu.

Bayanin ya ce an kai wanann samam ne bayan samun bayanan sirri dangane da kai komon mutanen da ake zargin cewa suna da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda, bayan tabbatar da lamarin, an kai farmaki tare da halaka su.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani harin ta’addanci da aka kai masu wasu masu yawan bude ne a garin na Jiza, inda aka kashe mutane 14 daga cikinsu, daga ciki kuwa har da ‘yan kasar Afrika ta gudu su biyu.

Kasar Masar dai ta fara fama da matsalolin tsaro ne tun bayan juyin mulkin da Abdulfattah Sisi ya yi tsohon shugaban kasar ta Masar.

3813150

 

 

 

captcha