IQNA

Sayyid Nasrullah: Ranar Quds Ranar Bijirewa Yarjejeniyar Karni

23:55 - May 26, 2019
Lambar Labari: 3483675
Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana ranar Quds ta wanann shekara da cewa rana ta kalubalantar yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillanicn labaran iqna, tashar talabijin ta Almanar ta bayar da rahoton cewa, a yammacin jiya Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah akasar Lebanon ya gabatar da jawabi, a kan zagayowar ranar 25 ga watan mayu, da ake tunawa ta ranar da sojojin Isra’ila suka arce daga kudancin Lebanon a 2000, bayan da suka sha wuta a hannun dakarun na Hezbullah.

A cikin jawabin nasa, sayyid Nasrullah ya tabo batutuwa da suke da dangantaka da halin da ake cikiayankin gabas ta tsakiya, musamman batun yunkurin da Amurka take yi tare da Isra’ila da kuma wasu daga cikin kawayensu na yankin musamman Saudiyya, da hadaddaiyar daular larabawa da kuma Jordan, inda suke shirin aiwatar da abin da suke kira yarjejeniyar karni.

Sayyid Nasrullah ya ce manufar yarjejeniyar karni ita ce amincewa da Isra’ilaa hukumance a tsakanin kasashen larabawa, da kuma fito da alakar da ke tsakaninsu a bayyane, sannan kuma a mayar da Falastinawa karkashin mulkin mallakar yahudawan Isra’ila da kuma amincewa da birnin quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila a hukumance.

Ya ce amincewa da wannan makirci da ake kitsa wa al’ummar Falastinu, babban cin amana ne ga al’ummar musulmi baki daya, wanda kuma abin takaici ne ana shirya hakan ne tare da wasu daga cikin manyan kasashen musulmi.

A kan haka Sayyid Nasrullah ya ce ranar Quds ta wanann shekara, za ta kasance ranar kalubalantar makircin da ake shiryawa al’ummar Falastinu da birnin Quds mai alfarma, makircin da ake kira da yarjejeniyar karni.

 

3814618

 

captcha