IQNA

An Kamamla Gasar Kur’ani A Aljeriya

23:02 - June 01, 2019
Lambar Labari: 3483697
An kammala gasar kur’ani mai tsarki ta duniya da aka gudanar a kasar Aljeriya tsawon mako guda.

Kamfanin dillancin labaran iqna, hukumar Radio da talabijin ta kasar Aljeriya ta bayar da rahoton cewa, an kawo karshen gasar kur’ani mai tsarki ta duniya da aka fara gudanarwa a kasar tun fiye da mako guda da ya gabata.

Wakilan kasashen duniya daban-daban ne dai suka halarci gasar, wadda aka saba gudanarwa a cikin kowane watan azumi.

Rayyanu Bin Ali da Abdulmajid Bin Ali sun na biyu , sharifa Almahawishi, da Muhammad Alhashimi sun zo an uku.

Tsohon shugaban kasar aljeriya Abdulaziz Butaflika ne dai ya kirkiro wanna gasa kimanin shekaru 16 da suka gabata, inda ake gudanar da ita a bangarori tilawa da kuma harda.

Daga karshe shugaban da kansa ne yak e bayar da kyauta ta musamman ga wadanda suka nuna kwazo a gasar, musamamn wadanda suka zo a matsayi na daya da na biyu da kuma na uku.

3816290

 

 

captcha