Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne jami’an tsaron gwamnatin yahudawan suka kai samame a gidan Ra’fat Nasif, daya daga cikin manyan jagorin kungiyar Hamas, a garin Tulkaram da ke gabar yamma da kogin Jordan.
Rahoton ya ce jami’an tasron gwamnatin yahudawan sun tafi da Ra’fat wani wuri da ba a sani ba.
Tun kafin wannan lokacin dai Isra’ila ta sha kama Ra’afat tana tsare a gidan kaso, inda ya kwashe kimanin jimillar shekaru 18 a gidan kason Isra’ila, kamar yadda a halin yanzu ma suka sake kame shi ba tare da tuhumarsa da aikata wani laifi ba.