IQNA

An Bukaci A Kawo Karshen Nuna Wa Musulmi Wariya A Jamus

23:58 - June 21, 2019
Lambar Labari: 3483761
Bangaren kasa da kasa, an kafa wani kwamiti na masana da ‘yan siyasa a kasar Jamus domin kalubalantar nuna wariya da kyama ga musulmi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai ae/article.24 ya bayar da rahoton cewa, Nina Muheh wata mai rajin kare hakkokin dan adam a kasar Jamus ta sanar da cewa, sun kafa wani kwamiti wanda zai mayar da hankali ga ayyukan nuna wariya da kyama ga musulmi da ke nuna ma suulmi a kasar da nufin kawo karshen hakan.

Ta ce wannan kwamiti ya hada da masu rajin kare hakkokin bil adama da kuma wasu ‘yan siyasa na kasar da suka hada har da ‘yan majalisar dokoki.

Cloudea Rout ‘yar mjalaisar dokokin Jamus daga jam’iyyar Green Party, da Christian Boholsten daga jam’iyyar masu sasaucin ra’ayi, suna daga cikin wadanda suka sanya hannu a cikin kwamitin.

Yanzu haka dai fitattun ‘yan siyasa 26 da kuma wakilan kungiyoyi farar hula masu fafutuka 37 ne suka sanya hannu tare da zama mamobin kwamitin, wanda yake neman a kawo karshen nuna kyama da muzgunawa ga musulmi a kasar a hukumance.

3821088

 

 

captcha