IQNA

Jagora: Shawarar Tattaunawa Da Amurka Ta Gabatar Yaudara Ce

23:45 - June 26, 2019
Lambar Labari: 3483773
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ne bayyana hakaa yau Laraba, yana maikara da cewa; Abin da Amukra take nufi shi ne kwance raba Iran da duk wasu makamai da take da su.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran juyin musuluncin wanda ya gana da tawagar ma’aikatar shari’a a yau Laraba ya ce; Muna yi wa Allah godiya cewa a cikin shekaru 40 na juyin musulunci al’ummar Iran ta sami daukaka ta hakika.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kara da cewa; Duniya ta tafi akan cewa babu yadda za a iya tilastawa al’ummar Iran ta rusuna ko a durkusar da ita, wanda hakan ya samo asali ne daga yunkurin da ya fara tun shekaru arba’in da su ka gabata.

AyatullahSayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Al’ummar Iran tana son daukaka ne da kuma cin gashin kanta da kuma ci gaba, don haka duk wani matsin lamba da azzalumai za su yi ba zai yi tasiri ba.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; Amurka wacce itace mafi sharrin gwamnatocin da ake da su a duniya, mai son zubar da jini ita ce take nunawa al’ummar Iran mai jarunta dan yatsan tuhuma, wanda hakan ba zai taba sanyawa ta ja da baya ba.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; Duk da cewa al’ummar Iran ce aka zalunta ta hanyar kakaba mata takunkumi, amma hakan baya nufin cewa Iran din tana da rauni.

Shugaban kasar Amurka ya sanar da kakaba sabbin takunkumai a kan kasar Iran, da nufin kara matsa lambaa kan kasar domin ta mika wuya ga manufofin Amurka.

Shugaban kasar ta Amurka ya bayyana cewa, sun saka takunkumi a kan jagoran juyin juya halin muslucni na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei da kuma ofishinsa, gami da wasu manyan jami’ai na ofishinsa, wanda hakan zai hana su ta’aummuli da kudade a Amurka.

ya ce wannan takunkumi zai takaice hanyoyin da jagoran juyin na Iran yake samun kudade da kuma manyan jami’ai da suke tafiyar da ofishinsa, kuma wannan zai kawo babbar illa ga ayyukansu.

Baya ga haka kuma shugaban na Amurka ya sanar da kakaba wasu takunkuman a kan wasu manyan kwamandojin rundunar kare juyin juya halin muslunci Iran, bisa abin ya kira hannun da suke da shi wajen gudanar da ayyukan kera makamai masu linzami na ballistic a kasar Iran, da kuma rawar da suke takawa wajen hana ruwa gudu a kasar Syria.

Haka nan kuma shugaban na Amurka ya ce manufar takunkuman ita ce matsa lamba kan Iran domin ta amince ta koma teburin tattaunawa da Amurka, kamar yadda kuma ya danganta batun da hana Iran mallakar makaman nukiliya.

A nata bangaren a ta bakin jakadan Iran majalisar dinkin duniya, wadannan matakai da Amurka take dauka suna a matsayin tozarta dokokin kasa da kasa, domin kuwa dukkanin matakan na Amurka a kan Iran babu wanda ya ginu a kan wata doka ta kasa wadda majalisar dinkin duniya ta amince da ita, bil hasali ma hakan ya yi hannun riga da dukkanin kudurorin majlaisar dinkin duniya.

Masana da dama sun yi imanin cewa, daukar wannan mataki da Amurka ta yi na kakaba sabbin takunkumai a kan kasar ba ya rasa nasaba da kakakbo jirgin leken asirin Amurka maras matuki da Iran ta yi a cikin wannan mako, wanda yake a matsayin babban abin kunya ga Amurka, wadda take bayyana wanann samfurin jirgin leken asiri a matsayin wanda ta yi amfani da kimiyyar fasaha ta kololowa wajen kera shi, tare da bugun gaba da ke kan cewa shi ne irinsa na farko a duniya, kuma babu kasar da ta mallake shi aduniya, amma da ya shiga cikin yankin Iran a wannan mako, Iran ta kakkabo shi cikin sauki.

Masana na ganin wannan lamari ya kunyata Amurka a idon duniya, domin kuwa Iran ta tabbatar wa duniya cewa abin da take fada kan shirinta na fuskantar duk wata barazana da gaske take yi, yayin da hakan a daya bangaren ya tabbatar da cewa Amurka tana kanbama kanta da makamanta da kayan aikinta fiye da kima, domin kuwa kakkabo jirgin leken asirin Amurka wanda babu irinsa a duniya da Iran ta yi, ya tabbatar da hakan.

Baya ga kunyata Amurka a kan wannan, a lokaci guda kuma abin da ya faru zai sanya sauran kasashe yin shakku kan abin da Amurka za ta fada a nan gaba kan makamanta da kuma ingancinsu da kuma tsarin kariyar da suke da shi, wanda hakan zai kawo mata koma baya ta fuskar cinikin makaman da take yi a duniya, wanda kuma a halin yanzu shi ne daya daga cikin manyan hanoyoyin da Amurka take samun kudaden shiga.

3822447

 

captcha