IQNA

Sheikh Zakzaky Na Bukatar Kulawar Gagagwa A Waje

23:47 - July 06, 2019
Lambar Labari: 3483809
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kare hakkokin musulmi ta kasar Birtaniya ta sake nanata cewa Sheik Zakzaky na bukatar kulawa ta musamman a wajen Najeriya.

Kamfanin dillanicn labaran iqna, cibiyar kare hakkokin musulmi ta IHRC da ke da mazauni a birnin London na kasar Birtaniya ta sanar da cewa, sakamakon gwaje-gwajen likitocin cibiyar ya tabbatar da cewa Sheikh Zakzaky na bukatar a gaggauta fitar da shi daga kurkuku domin yi masa magani.

Bayanin cibiyar ya ce dukkanin liktocin da suka gudanar da gwaje-gwajen jinin Sheikh Zakzaky da dauka watanni uku da suka gabata, sun bayyana cewa akwai bukatar daukar matakin gaggawa domin kula da lafiyarsa, sakamakon yadda guba ta yadu a cikin jininsa, wanda kuma hakan na bukatar kulawa a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na musamman a wajen Najeriya.

Daya daga cikin likitocin ad suka gudanar da gwajin jinin Sheikh Zakzaky a Chelsea a kasar Birtaniya mai suna Dr. Suhail Hassan ya bayyana cewa, sakamakon da suka samu yana da matukar hadari ga makomar lafiyar Sheikh Zakzaky.

Yanzu haka dai magoya bayan Harkar muslunci na ci gaba da yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta bayar da dama domin fitar da malamin zuwa wajen kasar domin duba lafiyarsa da kuam yi masa magani.

3824743

 

captcha