IQNA

Isra’ila Na Shirin Hade Yankunan gabar Yamma Da Kogin Jordan

22:46 - July 14, 2019
Lambar Labari: 3483837
Rahoton majlaisar dinkin duniya ya yi ishara da cewa Isra’ila na shirin hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan da yankunan da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa, a cikin rahoton da babban jami’in majaisar dinkin duniya kan harkokin Palestinu da Isra’ila Mike Link ya bayar, ya tabbatar da cewa Isra’ila da shirin kwace sauran yankunan falastinawa na gabar yamma da kogin Jordan, domin hade su da sauran yankunan da ke karkashinta.

Ya ce hakaika take-taken Isra’ial a cikin yan lokutan nan suna daga hankali, musamman yadda take ta kara yawan matsugunna yahudawa  acikin yankunan falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Mike ya kara da cewa, jami’an gwamnatin Isra’ila sun furta cewa nan bad a jimawa ba za su aiwatar ad shirinsu an kwace sauran yankunan falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan domin hade su da sauran yankunanta.

Bisa ga dokar majalisar dinkin duniya yankunan gabar yammada kogin Jordan an falastinawa ne, kuma gina duk wani matsugunnin yahudawa a cikinsu ya sabawa doka.

Yanzu haka yahudawan yan share wuri zauna kimanin dubu 640 a cikin matsugunnai 196 da Isra’ila ta gina a cikin yankunan falastinawa da ek gabar yamma da kogin Jordan.

3826964

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha